Talata 2 Yuni 2026 - 21:45
Koyarwar Ghadir Ta Ƙarfafa Tushen Rundunonin Gwagwarmaya A Duniyar Musulunci

Hauza/ Hujjatul Islam wal Muslimin Akhtari, yayin da yake jaddada alaka mai zurfi tsakanin al'adun Ghadir da rundunonin gwagwarmaya, ya bayyana cewa: "Muƙawama umarni ne na Alƙur'ani kuma tana da tushe daga mazhabar Ahlul Baiti (A.S), kuma abubuwan da suka faru a Falasɗinu da Lebanon sun nuna cewa tsayuwa a gaban zalunci da mulkin mallaka ita ce kadai hanyar kiyaye mutuncin al'ummar musulmi da tabbatar da manufofin Ghadir."

A cewar rahoton wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Hauza daga Mashhad, Hujjatul Islam wal Muslimin Muhammad Hassan Akhtari, Shugaban Hai'ar Amintattu ta Majalisar Ahlul Baiti (A.S) ta Duniya, a yau Talata 12 ga watan Khordad (02 ga Yuni), a wurin Taron Ƙasa da Ƙasa na Biyu kan "Ghadir da Muƙawama" wanda aka gudanar tare da halartar masana na fagen ilimin addini, jami'o'i, da al'adu na ƙungiyoyin muƙawama a Hubbaren Imamzadeh Yahya bin Zaid (A.S) da ke Mashhad, yayin da yake taya murna da zagayowar kwanaki goman Wilaya da Imamanci, ya jaddada alaka mai zurfi da ke tsakanin al'adun Ghadir da kuma rundunonin gwagwarmayar Musulunci.

Ghadir; Ranar Tabbatar da Jagorancin Allah Ga Al'ummar Musulmi

Yayin da yake nuni da girman waki'ar Ghadir, ya bayyana cewa: 'Idin Ghadir mai albarka, rana ce ta kafa halifanci, ayyana wanda zai gaji Manzon Allah (S.A.W.A), da kuma gabatar da Imami kuma jagoran al'ummar musulmi daga bangaren Allah Madaukakin Sarki. Don haka, ina taya daukacin musulmi, mabiya shi'a da masoya Ahlul Baiti (A.S) murnar wannan babban biki."

Shugaban Hai'ar Amintattu ta Majalisar Ahlul Baiti (A.S) ta Duniya ya kuma girmama tare da tunawa da shahidan Musulunci, na gwagwarmaya, da na Juyin Juya Halin Musulunci, inda ya ce: "A yau ma a Lebanon, Falasɗinu, da sauran yankuna na rundunonin gwagwarmaya, mujahidai da dama suna yin shahada a tafarkin kare Musulunci da fuskantar zalunci da mamaya, kuma hanyar shahidai tana nan tana ci gaba."

Yayin da yake nuni da falalolin Amirul Muminina Ali (A.S) a cikin tushen littattafan Musulunci, ya kara da cewa: "Kamar yaddda manyan malaman tafsirin Musulunci suka fada, daruruwan ayoyin Alƙur'ani mai tsarki sun sauka ne game da falaloli da matsayin Amirul Muminina (A.S), haka nan kuma akwai hadisai masu yawa da aka rawaito daga Manzon Allah (S.A.W.A) da ke bayyana matsayin wannan bawan Allah."

Hujjatul Islam wal Muslimin Akhtari ya ci gaba da cewa: "Manzon Allah (S.A.W.A) a cikin hadisai da dama ya bayyana alaƙa mai zurfi da ke tsakaninsa da Amirul Muminina (A.S); daga ciki akwai mashahurin hadisin nan da ke cewa: "Ya Ali, kai daga gare ni kake, ni ma daga gare ka nake" (Ya Ali anta minni wa ana minka), wanda hakan ke nuna dunkulewar tafarki, manufa, da sakon Manzon Allah (S.A.W.A) da na Amirul Muminina (A.S)."

Ya bayyana gwagwarmaya a matsayin wani tabbataccen sashe na Alƙur'ani, inda ya jaddada cewa: "Gwagwarmaya ba wai kawai wata dabarar siyasa ba ce, a'a, umarni ne na Allah filla-filla a cikin Alƙur'ani. Al'adun gwagwarmaya sun samo asali ne daga cikin koyarwar Alƙur'ani mai tsarki da mazhabar Ahlul Baiti (A.S), kuma a yau ana kallonta a matsayin wani samfuri mai nasara a duniya."

Shugaban Hai'ar Amintattu ta Majalisar Ahlul Baiti (A.S) ta Duniya ya bayyana cewa: "Abubuwan da suka faru a shekarun baya sun nuna cewa sulhu da tattaunawa da haramtacciyar daular sahyoniyawan Isra'ila ba su iya samar da hakkin al'ummar Falasɗinu ba, amma gwagwarmaya ta sami nasarar sauya lissafin yankin, sannan ta sanya maƙiya cikin mawuyacin hali da kalubale na gaske."

Yayin da yake nuni da nasarorin da rundunonin gwagwarmaya suka samu a shekarun nan, ya ce: "Gwagwarmayar Musulunci a Falasɗinu da Lebanon ta sami nasarar durkusar da daular sahyoniyawa a gaban zabin al'ummomin yankin, sannan ta samar da gagarumin ikon tunkara da kariya."

Hujjatul Islam wal Muslimin Akhtari ya kara da cewa: "A yau al'ummomin duniya masu neman 'yanci sun fi kowane lokaci gane tasiri da amfanin rundunonin gwagwarmaya, kuma suna kallon wannan tafarki a matsayin hanyar tunkarar zalunci, mamaya, da neman mamaye kasashe."

Ci Gaban Tafarkin Wilaya A Cikin Rundunonin Gwagwarmaya 

A ƙarshe ya jaddada cewa: "Gwagwarmayar Musulunci ita ce ci gaban tafarkin wilaya da tsawaituwar hanyar da aka zana a Ghadir. Kamar yadda Alƙur'ani mai tsarki yake kiran muminai zuwa ga tsayuwa a gaban maƙiya, su ma rundunonin gwagwarmaya ta hanyar yin koyi da al'adun wilaya da koyarwar Ahlul Baiti (A.S), suna tsaye a gaban maƙiyan Musulunci, kuma wannan tafarki zai ci gaba da daukaka tare da ƙarfi."

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha